MUHIMMANCIN AIKIN SA KAI A TSAKANIN AL’UMMA DOMIN INGANTA MUHALLI
Jawabin
Dr. Nura Muhammad
a taron
Gangamin Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Da Inganta Muhalli a Garin Hadeja
Lahadi 18 ga Agusta, 2019
A’uzubillahi Minash shaid’anir rajim. Bismillahir rahmanir raheem.
Maimartaba Sarkin Hadeja, kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa; Alhaji (Dr) Adamu Abubakar Maje Haruna (CON)
Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa; Alhaji Umar Namadi
‘Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar yankin Arewa maso gabas na Jihar Jigawa; Sanata Ibrahim Hassan Hadeja (Shattiman Hadeja II)
Babban Sakatare a Ma’aikatar kula da Muhalli ta Jihar Jigawa; Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa
Shugaban Hukumar Talabijin ta Jihar Jigawa; Alhaji Ishaq Hadeja
Shugaban K’ungiyar Gangamin Tsabtace Garin Hadeja da Shuka Bishiyoyi (HGPE); Mallam Ahmad Ilallah
Wakilan Kungiyar Inganta Muhalli da Shuka Bishiyoyi ta garin Gumel (GCIGCE)
Shugabannin Kungiyoyin sa kai na al’ummar Hadeja
Sauran manyan bak’i da aka gayyata
‘Yan Jarida na rediyo, da talabijin, da jaridu, da kuma kafafen sada zumunta na zamani
Y’anuwana maza da mata
Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barakatuhu….
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Mad’aukakin Sarki, mai kowa mai komai, da ya bamu ikon taruwa a yau domin gudanar da wannan gagarumin aiki na alheri. Tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon tsira Annabi Muhammad (SAW), fiyayyen halitta kuma mafificin masu tsabta da inganta muhalli.
Daga farko, zan fara da godiya maras adadi ga shugabannin wannan gamayya ta matasa domin tsabtacewa da kuma inganta garin Hadeja da suka bani wannan muhimmiyar dama har kashi biyu.
Ta farko ita ce kasancewa babban mai gabatar da jawabi a matsayina na d’an uwansu matashi – Dr Nura. Domin a ba mutum damar yin magana gaban irin wannan gangami, musamman idan a ka yi la’akari da irin mutanen da aka tara a wannan wuri, to ba k’aramar dama ba ce da kuma girmamawa.
Maudu’in da a ka ce na yi magana a kansa shine ‘Muhimmancin Aikin Sa kai a Tsakanin Al’umma Domin Inganta Muhalli’.
Dama ta biyu kuwa ita ce, ta alfarmar da aka yi wa Gidauniyar da na k’irk’ra, wato Gidauniyar Unik Impact (ko Unik Impact Foundation a turance) ta yin tarayya a wannan aikin alheri da suka assasa ta hanyar ba da gudunmuwar d’aruruwan irin mad’aci da kuma mangwaro na zamani. Babban abin godiya ne a ba ka damar shiga cikin wani aikin alheri na al’umma.
Shuka bishiya abu ne mai matuk’ar muhimmanci a garemu ba wai kawai ta fuskar kariya da inganta muhalli ba, a’a, har ma ta fuskar addininmu, tattalin arzik’inmu, da kuma walwalarmu.
Tun farko, shi dai addinin musulunci, a matsayinsa na tsarin wayewa na gabadayan rayuwa, ya yi tanadin tsare-tsare da ka iya magance matsaloli na muhalli da ke yi wa d’an adam barazana a wannan lokaci. A bisa tarbiyya irin ta addinin musulunci, wasu magabatan na kallon cewa hatta shi kansa muhallin wani nau’ine na amana da Allah (SWT) ya mallaka a hannun bayinSa. Akwai ayoyi da dama na Alkura’ani mai tsarki da su ke tsawatarwa ga mumunai akan almubazzaranci, yad’a 6arna da kuma fasadi a bayan k’asa. Lalatawa da kuma wofintar da muhalli, tamkar wani nau’ine na almabozaranci da kuma 6arna a bayan k’asa.
Saboda matukar muhimmancin da addinin musulunci ya dora kan amfanin itatuwa a muhallin dan Adam shi ya sa ma ya yi hani da sare bishiyoyi da sauran nau’in shuke- shuke ba tare da wani kwakkwaran daliliba.
Manzon Allah Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, ya kwadaitar a cikin ingattattun hadisansa akan falala da kuma fa’idar inganta muhalli, da daraja shi, da kare shi ta hanyar shuka bishiyoyi. D’aya daga cikin hadisan shine wanda mazon ya ke cewa; “ita duniyar nan koriya ce shar k’yak’yk’yawa, kuma Allah (SWT) ya dank’a muku ita a matsayin amana”.
Ko da a yanayi irin na yak’i, Manzon tsira ya kan gargadi kwamandojin rundunonin musulmi da su guji sare bishiyoyi da kuma amfanin gona na abokan gaba. Ma’aikin dai ya kasance a lokacin rayuwarsa yana bada muhimmanci da karfafa guiwa kan amafani da k’asa mai d’orewa, rage tara shara, da kuma jin k’ai ga dabbobin daji. Cikamakin annabawan, ya samar da ‘Hima’ a kudancin birnin Madina, inda ya haramta yin farauta a cikin tsawon kusan murabba’in kilomita bakwai (7). Ya kuma hana sare bishiyoyi a cikin tsawon kusan murabba’in kilomita ashirin (20). Allahu Akbar. Allah muna k’ara gode maka a bisa ni’imar addinin musulunci da ka yi mana.
Shuka bishiya wani nau’i ne na sadaka, kamar yadda ya zo a hadisi. Imamu Bukhari ya rawaito a wani hadisi a cikin littafinsa cewa Manzon Allah (SAW) ya ce; “Duk wani musulmi da ya shuka bishiya, kuma wani bil adama ko dabba ta ci daga jikin wannan bishiyar, to za a saka ma sa ne tamkar ya ba da sadaqa” (Sahih Bukhari Vol. 8, Book 73, No. 41)
Wad’annan ayoyi da kuma hadisai na Mazon tsira na nuni da cewa, shi dai wannan addini na mu na musulunci, shine tsarin wayewa na farko a duniyar nan da ya fara rubutawa da kuma zaburar da d’an adam akan tanade tanaden Kimiyyar muhalli, da inganta shi, da kuma kare dabbobin daji. Kula da muhalli dai na mu ne musulmai ba wai na wani bature ba ne ko iliminsa. Tun dai kafin a haifi magabatan mai sabulu balbela ke da farinta tas-tas!
A kimiyyance kuwa, bishiya ce ke bamu sinadarin Oxygen (O2) na iskar da mu ke shak’a. Sannan ita kuma ta janye na Carbon dioxide (CO2) da mu ke fitarwa. Bishiya ce ke rage abubuwa ma su wari da kuma gur6ata yanayin iska kamar sinadaran nitrogen oxide, ammonia, sulfur dioxide da kuma ozone. Bishiya ta na k’arfafa k’asa ta rage zaizayewarta. Bishiya ta na sanyaya tituna da gidajenmu su zama masu ni’ima. Bishiya tana taimkawa wajen rik’e lema a cikin k’asa. Bishiya na kare yara daga hasken rana na ultra violet mai cutar da fatarsu. Bishiya tana samar da abinci ga mutane da dabbobi.
Bishiya na kawo waraka a wasu nau’o’in rashin lafiyar jiki da kuma k’wak’walwa. Yawan Bishiyoyi na rage tashe-tashen hankula a tsakankanin al’umma. Bishiya tana bun’kasa tattalin arzik’in al’umma. Bishiya tana samar da makamashi. Bishiya tana k’ara darajar kadarar gida, ko gona, ko kuma fili a lokacin sayar da shi.
Kuma sare bishiyoyi ne ke jawo karuwar d’umamar yanayi, kwararowar hamada, zaizayar k’asa, rashin albarkar noma da yawan ambaliyar ruwa, ga kuma rashin muhallin zama ga namun daji, da wahalar ruwan sha.
A kowace shekara, hamada na k’ara kwarara zuwa kudu daga arewa da nisan kusan kashi shida na kilomita d’aya. Kamar dai, a bisa misali, hamadar na tafiyar nisan da ya kai daga nan zuwa garin Mallam Madori a cikin kowane shekaru talatin (30). Kwararowar hamada kuwa na daga gaba gaba a cikin abubuwan da ke kawo tsadar abinci, k’arancin ruwa na sama da na k’asa, tashe-tashen hankula a kan guraben noma da kiwo, tilastawa mutane yin k’aura, da kuma k’aruwar talauci a tsakanin al’umma.
Jiharmu ta Jigawa na d’aya daga cikin jihohi uku a Najeriya da su ke a kan gaba wajen fuskantar barazana ya kwararar hamada.
Amma kash, duk da wad’annan fa’idodi na shuka bishiya da kuma kare muhalli da addini ya nusar da mu akan su, da kuma ta fuskar tattalin arziki da zamantakewarmu, sai ga shi cewa, mu dai an shuka bishiya ba mu shuka ba. Mun kuma sare bishiya ba mu shuka ba!
Jama’a, mecece mafita a nan?
MafIta dai ta farko ita ce cigaba da wayar da kan al’ummarmu akan amfanin shuka bishiya da tattalinta, da kuma maida hankali wajen kokarin dakatar da kwararowar hamada. Wadanda ke da alhakin gabatar da wannan aiki na wayar da kan jama’a dai ba su wuce gwamnati ba, da maluman addini, da kuma k’ungiyoyi na al’umma ma su zaman kansu. Wato tamkar dai irin abin da mu ke yi a yau d’in nan.
Mafita ta biyu kuwa ita ce samar da makamashi mai sauk’in kud’i da samu ga al’umma. Abu ne da kowa ya sani cewa babban abin da ya ke kawo yawan sare bishiyoyi a wannan 6anagare na mu ita ce bukatar itace don yin makamashi. A saboda haka, da alama fa mutane za su iya ci gaba da cinye dazuzzukan nan idan har ba a samar mu su da wani makamashi a madadin itacen ba. Itace dai kusan shine makamashin da a yau bai fi k’arfin da yawa daga cikin al’ummarmu ba, kuma a kan same shi ba da wata wahala ba. A gaskiyar magana, har sai an samarwa da al’umma wani makamashi kwatankwacin irinsa ne za a iya yin wata tabbatacciyar magana akan hana saran bishiyoyi domin yin makamashi da su.
Mafita ta uku kuwa ita ce al’umma su tashi tsaye a d’aid’aiku da kuma a k’ungiyance ko kuma a gwamnatance su shuka bishiyoyi. Ina matuk’ar farin cikin cewa wannan shine dalilin taruwarmu gaba d’aya a wannan fili.
Shi fa wannan mataki na tattara kan al’umma su yi ta shuka bishiyoyi ba bak’on abu bane a cikin al’ummar nan. Mun bud’i ido a garin nan mun ga ana yin irin wad’annan gangami. Mun kuma tashi mun ga garin nan gaba d’ayansa a kewaye da rukunin bishiyoyi daban daban da ake kira plantation, gwanin ban sha’awa. Don haka, yanzu ne lokacin da za a komawa baya a yi karatun ta-nutsu, ba wai gobe ko jibi ba.
Saboda a daidai lokacin da mu ke yin wannan zancen, wa su k’asashen fa, hatta a nan nahiyarmu ta Afrika, tuni sun yi nisa a cikin wannan al’amari. A cikin watan Yulin da ya gabata, K’asar Habasha (wato Ethiopia), wadda ke da yawan jama’a kimanin miliyan tamanin (80), wato kwatankwacin kaso d’aya bisa uku kenan na yawan al’ummar Najeriya, ta yi wa al’ummarta k’aimi su ka shuka bishiyoyi kimanin miliyan d’ari uku da hamsin da uku (353). K’asar ta samu nasarar shuka wad’annan bishiyoyi masu dimbin yawa ne a rana d’aya tak a k’ark’ashin wani shiri na musamman na korar hamada da matashin Fira-Ministan k’asar, Abiy Ahmed Ali, ya jagoranta da kansa.
Babu abin da zai hanamu irin wannan yunk’uri anan Najeriya koma a gida Jihar Jigawa. Domin shi fa shuka bishiyar nan,
nagge ne dad’i goma; ga lada, ga samar inuwa, ga hana k’wararowar hamada, ga kuma, uwa uba, arzik’i.
Allah ya ja zamanin Sarki, manyan bak’i, ina da masaniya akan wani nazari mai ban al’ajabi da wani kamfanin bincike na k’wararru da ke birnin London mai suna Price WaterHouse Cooper ya ke gudanarwa a halin yanzu. Shi dai wannan nazarin bincike ana gudanar da shi ne kacokam akan irin arzikin da ke mak’are a jikin bishiyar charbi ko kuma maina. A binciken, wanda har yanzu ba a fito da shi ba, k’asar India ta na da irin wannan bishiya guda miliyan ashirin (20) kacal. Amma wannan bishiyoyi ta na samarwa da k’asar kud’ad’en shiga kusan dalar Amurka biliyan shida (6Billion) a kowace shekara.
Binciken ya cigaba da nuna cewa, k’asar Najeriya mai bishiyar maina miliyan d’ari da talatin da hud’u (134), ita ce ta fi kowace k’asa albarkar wannan bishiya a fadin duniya. Jihar Jigawa kuwa ita ce a kan gaba a fad’in Najeriyar da yawan bishiyoyi miliyan talatin da hud’u (34). Wato jihar Jigawa ita kad’ai ta na da bishiyoyin maina sama da d’aya da rabin na k’asar India. Amma babban abin tak’aici a nan shine, ita Najeriya kwatankwacin dalar Amurka miliyan d’ari hud’u da arba’in (440) kawai ta ke iya samu a jikin wad’annan bishiyoyi a duk shekara!
Ni dai a guna romon wannan bincike shine, idan mu ka dage, jiharmu ta Jigawa za ta iya samun ak’alla dalar Amurka biliyan d’aya (wato kusan Naira biliyan 360 kenan a kowace shekara) daga jikin wad’annan bishiyoyi da Allah ya albarkacemu da su. Naira biliyan 360 dai ya fi kwatankwacin duka kud’in da jihar ke samu a cikin shekara daga gwamnatin tarayya. Haka dai irin wannan gara6asa da sirri ke a cikin bishiyar k’aro, wanda namu na nan Jigawa da Yobe shine giredin farko a duk fad’in duniyar nan.
Za mu iya zage dantse kamar k’asar Habasha mu shuka miliyoyin wad’annan bishiyoyi. Za su yi mana maganin kwararowar hamada, sannan, uwa uba, su azurta al’ummarmu da arzik’i mai d’orewa.
Da alama dai niyyar irin wannan zage dantse ne samari matasa su ka fara yi a yau d’in nan. Yunk’uri ire iren wannan daga bangaren matasanmu, wad’anda kuma su ne gobe, ya sa na ke cike da fatan cewa in Allah ya yarda goben ta mu a bisa ga dukkan alamu za ta kasance mai k’yau.
K’ungiyoyi ne biyu masu zaman kansu, na samari (d’aya a garin Gumel d’aya kuma a Hadeja), su ka yi tarayya a kan muradi na kula da kuma inganta muhalliasu, ba tare da cewa kowace d’aya ta san da zaman d’ayar ba. Ni kuma ta hanyar kafar sada zumunta ta facebook na yi muwafak’ar haduwa da su har mu ka k’ulla zumunta mai ak’ida da manufa iri d’aya. D’aya daga cikin manufofi da ak’idun Gidauniyar da na k’irk’ra (wato Unik Impact) shine taimakon al’umma ta ji6intar harkokin ilminsu, kiwon lafiya, tattalin arziki da kuma inganta muhallinsu. To a wannan ga’bar ne k’udiri da manufofinmu su ka zo d’aya.
Wannan ita ce goben da mu ke fatan samarwa a tsakanin al’ummarmu. Kuma ita ce goben da a kullum iyayen k’asa sarakuna ke jan hankulanmu a kai. Sannan ita ce goben da a cikinta mu ke fatan al’umma gaba d’ayanta za ta gina siyasarta kacokaf a kan doron cigaba, ba tare da yin la’akari da wasu bambance bambance na ra’ayin jama’iyya, ko 6angare ko kuma na jinsi ba.
Babu shakka dole ne sai al’umma ta kawar da duk wani nau’i na son rai, ta kuma ci gaba da yin irin wannan tarayyar akan muhimman abubuwan da su ka shafe ta, musamman na harkar ilminta, da lafiyarta, da kuma tattalin arzik’inta ne kawai, za ta iya gamon da katar da ci gaba mai dorewa
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dai ya ce: “Mafi alkhairi a cikin al’umma shine wanda ya amfani al’ummar.”
Allah ka sa mu ci gaba da zama masu amfani ga al’ummarmu baki d’ayanta
Assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wa barakatuhu…
coming soon!