Saratu Garba Abdullahi, from Birnin Kudu Local Government in Jigawa State, a PhD student of St Luios University in Saint Louis, Missouri, United States is one of the beneficiaries of Unik Impact Foundation’s special scholarship based on merit and scholarly achievements. She is a beacon of hope and inspiration for all girls across our state.
Saratu is a model of the future we hope to create for every girl child; a future of virtues, hardwork, opportunities and eventually empowerment.
Like the millions of girls we seek to inspire, Ms Abdullahi attended the Central Primary School in her native Birnin Kudu and then later Government Girls Secondary School Gwaram in Jigawa State. A General Nurse,
Midwife, and a
Nursing Educator, she is also proudly a holder of both Bachelor of Nursing Sciences and MSc. Community Health Nursing from the Teerthanker Mahaveer University Moradabad India. She holds an MBA from the Maryam Abacha American University of Niger.
She is an SLU Missouri trained Cognitive Behaviour and Cognitive Stimulation Therapist and is currently into MSc Social Works at the University of Missouri
We congratulate Abdullahi, a University Lecturer with the College of Health Sciences Bayero University Kano and a beacon of opportunities and hope of international repute.
Unik Impact Foundation is honoured to be part of Saratu’s awesome and rare success story.
Unik Girls: Tallafin Karatu Na Musamman A K’asashen K’etare
Saratu Garba Abdullahi, y’ar asalin K’aramar Hukumar Birnin Kudun Jihar Jigawa, mai nazarin digirin digirgir (PhD) a Jami’ar St Louis da ke Missouri a k’asar Amurka, ta na d’aya daga cikin wad’anda su ka yi nasarar samun tallafin karatu a k’asashen k’etare na Gidauniyar Unik Impact a bisa cancanta da kuma tarin karatu da Allah SWT ya sahale ma ta. Saratu dai tamkar wata fitulace abar koyi ga dukkanin yaranmu mata dake fad’in Jiharmu da ma k’asa ba ki d’aya
Ita ce irin goben da mu ke fatan samarwa ga dukkanin y’anmatan mu; goben kame kai, zage dantse, dama, da kuma dogaro da kai
Kamar dai da yawa daga cikin yaranmu, Ms Abdullahi ta fara karatunta a Central Primary School da ke mahaifarta a garin Birinin Kudu, sannan ta wuce zuwa Makarantar Sakandiren Mata ta Gwamnati da ke garin Gwaram dukkaninsu a Jihar Jigawa. Ma’aikaciyar Jinya (Nurse), k’wararriyar Ingozoma (Midwife), Kuma malamar karatun jinyar, ta samu takardar digirin ta na farko da na biyu duk a 6angaren jinya (Nursing) daga Jami’ar Teerthanker Mahaveer University da ke Moradabad a k’asar India. Ta kuma k’ara da karatun sarrafa kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha da ke k’asar Niger.
Ta samu takardar shedar horo na musamman a kan dabarar canja yanayin tunani da kuma halayyar bil adama domin samun sauk’in wasu nau’o’i na rashin lafiya (CBT & CST), dukkaninsu a Jami’ar ta St Louis. Ta kuma share fili ta fara sabon digiri na biyu akan aikin kula da zamantakewa (MSc Social Works) shi kuma a Jami’ar Missouri duk dai a can Amurkan
Muna taya Hajiya Saratu murna, malamar Jami’ar Bayero a tsangayar Karatun Kimiyyar Lafiya kuma babbar abun k’watance a ko ina cikin fad’in duniyarnnan.
Abun alfharine da kuma karramawa a gun Gidauniyar Unik Impact kasancewar mun samu alfalmar shiga labarin rayuwar wannan fitacciyar baiwar Allah