Zakar Muhammad Kani, from Hadejia Local Government in Jigawa State, a Bechalors Degree holder in Information & Communications Technology from Esep Le Berger University in Benin Republic and Informatics Academy of Singapore is one of the beneficiaries of Unik Impact Foundation’s special foreign scholarship based on merit
A beacon of inspiration for our youths across the State, Unik Impact Foundation is honoured to be part of his success. He is a model of the future of opportunities we hope to create for everyone who desires it. A future of hardwork, virtue, perseverance and ultimately empowerment and independence
Mr K’ani, a typical neigbourhood young man who attended Shamsuddeen Islamiyya Primary School and Government Secondary School Wunti all in Hadejia, is also holder of International Advanced Diploma in Computing from the Informatics Academy of Singapore. He has a Graduate Certificate in Project Management and Proficiency Certificate in British Project Management both under British Project Management Body of Knowledge (PMBOK). Additionally, he trained in Health Safety & Environment at levels 1,2&3 under the British Safety Organisation and Human Resources Management at the Institute of Art Management and Professionals
With a Certificate in Network and Cybersecurity from Sky7 Training and Consulting India, Zakar has skills in network cabling, network and CCTV installations, cybersecurity, PC maintenance and database management
We congratulate Mr K’ani, an Intern in the Studios of SAWABA Radio Hadejia, as he sets out to leverage on future opportunities and inspire millions
Unik Scholars: Tallafin Karatu Na Musamman A K’asashen K’etare
Zakar Muhammad Kani, haifaffen Hadejan Jihar Jigawa, wanda ya yi karatunsa na digirin farko a kan fashar sadarwa da yad’a bayanai (Communications & Information Technology) daga Jami’ar Esep Le Berger a Janhuriyar Benin da kuma Makarantar Nazarin Sadarwa da ke k’asar Singapore, ya na d’aya daga cikin wad’anda su ka yi nasarar samun tallafin karatu na musamman a k’asashen k’etare na Gidauniyar Unik Impact a bisa cancantarsa
Gidauniyar Unik Impact na alfahari da alfarmar kasancewa cikin nasarar wannan abun k’watance ga matasanmu a fad’in Jihar Jigawa. Sune dai irin goben da mu ke fata a kan kowane matashin da ya tashi tsaye ya kuma jajirce. Goben aiki tuk’uru, yakana, zage dantse, da dama da kuma dogaro da kai
Mallam Zakar wadda ya fara karatu a Shamsuddeen Islamiyya Primary School da kuma Makarantar Sakandare ta Gwamnati ta Wunti duk a garin Hadeja, ya samu shaidar babbar diploma a kan sarrafa na’ura mai k’wak’walwa (Adanced Diploma in Computing) daga Makarantar Nazarin Sadarwa da ke k’asar Singapore. Ya kuma samu shaidar horo akan Kula da Ayyuka (Project Management) da kuma wata shaidar ta k’warewa akan Kula da Ayyuka ta kasar Birtaniya) dukkaninsu a k’ark’ashin British Project Management Body of Knowledge (PMBOK). Haka kuma ya samu horo a matakai na 1,2&3 a kan Lafiya, Kariya, da kuma Muhalli (Health Safety & Environment) a k’ark’ashin gamayyar kare kai ta k’asar Birtaniya (British Safety Organisation), da kuma k’arin wani horon a kan iya sarrafa ma’aikata (Human Resources Management) a k’ark’ashin Institute of Art and Management Professionals.
Zakar na da satifiket d’in sa na nazarin hana kutse cikin yanar gizo da hanyoyin sadarwa (Certificate in Network and Cybersecurity) daga Sky7 Training and Consulting India. Kuma ya kasance ya na da dabarun shimfid’a hanyoyin sadarwa (Network Cabling), mak’ala na’urorin d’aukan bayanai (CCTV Installations), hana kutse cikin yanar gizo (Cybersecurity), kula da na’ura mai k’wak’walwa (PC Maintenance) da kuma kula da rumbun bayanai.
Muna jinjinawa wannan matsahi, wadda a yanzu ya ke aiki a d’akin shirye shirye na Rediyon SAWABA da ke Hadejia. Muna kuma fatan zai samu wasu damarmakin a nan gaba ya kuma ci gaba da kasancewa abun k’watance a cikin al’umma