Musa Musa (not real name), is an 18months old baby who had third degree burns involving the scalp, his face, lips and eyes. He needed hundred of thousands for multi stage special plastic surgery and oculoplasty procedures. He is alreday through with the first stage of both and is looking comfortable in his mother’s arms
Unik Impact Foundation profusely thanks Dr Usman Muhammad, an Opthalmology trainee with Aminu Kano Teaching Hospital who presented us with the rare opportunity to add value to the youngster and most importantly congratulate Musa and his family for a successful start. We wish him all the best and Allah’s continues guidance as he faces the next stages of his delicate surgeries
#ItIsAllAboutOpportunities
#DamaceKawai
#Compassion
#unikHealth
www.unikimpact.foundation
Musa Musa (ba sunan gaske ba), yarone da ke shan nono mai kimanin watanni 18 wanda Allah SWT ya jarabta da mummunan k’una na wuta da ya shafi dukkanin k’waryar kansa, da fuska, da ido da kuma le66a. Ya shiga yanayin da ya ke buk’atar d’aruruwan dubbai na nairori domin wasu aiyukan tiyata na musamman a matakai dabam dabam. Cikin ikon Allah dai har ya samu nasarar gama matakin tiyatarsa na farko, kuma har ya fara walwala da wasanni irin na yara a hannun mahaifiyarsa
Unik Impact Foundation na godiya maras iyaka ga Dr Usman Muhammad (likita mai nazarin k’warewa a harkar ido a babban asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano), wadda ya fara kawo mana wannan damar ta shiga cikin rayuwar Musa. Mu na kuma taya Musa da iyayensa murnar samun wannan nasara a matakin aiki na farko, da kuma yi mu su fatan alheri da kuma addu’a akan sauran matakai na wannan tiyata mai wahalar gaske da ke gabansu
#DamaceKawai
#ItIsAllAboutOpportunities
#UnikHealth
www.unikimpact.foundation